Welcome, Guest: Register On Nairaland / LOGIN! / Trending / Recent / NewStats: 3,150,333 members, 7,808,171 topics. Date: Thursday, 25 April 2024 at 08:02 AM |
Nairaland Forum / Nairaland / General / Politics / Wakar Janar Muhammadu Buhari (4352 Views)
ْ / Press Statement By General Muhammadu Buhari On The School Certificate Issue / IBB Endorses Muhammadu Buhari For President - SaharaReporters (2) (3) (4)
Wakar Janar Muhammadu Buhari by bashali: 7:53pm On Jul 09, 2009 |
WAKAR JANAR MUHAMMADU BUHARI Bismillahi rabbana Allah Sai Janar Buhari Nai niyya in wake zakina Sai Janar Buhari In sai dashi gun duka dangina Sai Janar Buhari In san da su babu kamar nawa Sai Janar Buhari Zaben badi kam ni nai zabi na Sai Janar Buhari Tabbas ni Buhari zan zaba Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Yai gwamna yayi minista fa Sai Janar Buhari Har yai shugaban kasa nawa Sai Janar Buhari Amma bai ci mana amana ba Sai Janar Buhari Yayi riko da gaskiya baba Sai Janar Buhari Duk jama’a sunata madalla Sai Janar Buhari Janar Buhari Allah maimaita Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Jama’a na a basu mai sonsu Sai Janar Buhari Buhari kam ya amsa kiransu Sai Janar Buhari Har yai takara fa dominsu Sai Janar Buhari Aka sace kuri’arsu jarinsu Sai Janar Buhari Aka baiwa wani can barensu Sai Janar Buhari Yana ta barna fa da sunansu Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Janar Buhari yai kukan zucci Sai Janar Buhari Yana ta begen so da aminci Sai Janar Buhari Da rashin ruwanmu har da abinci Sai Janar Buhari Balle manya babu suturci Sai Janar Buhari Wannan ya hana masa barci Sai Janar Buhari Har sai ya kwato mana ‘yanci Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Matsalolinmu sun zame luru Sai Janar Buhari Ga barna kamar Karen zuru Sai Janar Buhari Ga sata I dogarin burgu Sai Janar Buhari Ga wasu ma suna ta dan daru Sai Janar Buhari Kasarmu ta ishe cikin turu Sai Janar Buhari An tura mu mun ishe garu Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari To dada sai muzo mu dau aniya Sai Janar Buhari Domin sabuwar dashen tafiya Sai Janar Buhari Don mun mantuwa gidan ajiya Sai Janar Buhari Ma jewa buhari ban gajiya Sai Janar Buhari Mu tuna mai yazo muna ta jira Sai Janar Buhari Bana kam bamu yin irin ta jiya Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Janaral sai ka zo ka cecemu Sai Janar Buhari Wahala ta saka mu mun dimu Sai Janar Buhari Bamu ganin abinda ke binmu Sai Janar Buhari Kokuwa wanda ma fa zai karmu Sai Janar Buhari Kowa na ta so ya cucemu Sai Janar Buhari Ba me son ya san bukatunmu Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Ina da zargin da akwai azama Sai Janar Buhari A kau da zaben badi kan niyya Sai Janar Buhari Ko kuma a kauce shirya zabenma Sai Janar Buhari Domin kar buhari yai nasara Sai Janar Buhari To wallahi bar batun wasa Sai Janar Buhari In ta kasance zan dau fansa Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Ya ahalin Najeriya dangi Sai Janar Buhari Dole muzan muna gudun kangi Sai Janar Buhari Ko da za mu zammuna bangi Sai Janar Buhari Koko muna rawar kidan gangi Sai Janar Buhari Tabbas yazzamo musa waigi Sai Janar Buhari Ko ma samu me jikin kirgi Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Ina kuke ku masu bidar suna Sai Janar Buhari Yadda kasan ana zuben zana Sai Janar Buhari To haka za mu tashi har kwana Sai Janar Buhari Kullum kan idonku sai yana Sai Janar Buhari Komai ko budewar rana Sai Janar Buhari Sai kun ja ciki kamar tana Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Ya dangi mu dauki butoci Sai Janar Buhari Mui sallah don maganin kunci Sai Janar Buhari Mun farka da zamanin barci Sai Janar Buhari Kuma mu kula mu kauce ganganci Sai Janar Buhari Nasara kam abarmu sai mun ci Sai Janar Buhari Tabbas sai mun daga tutoci Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Kasarmu ta zame cikin rami Sai Janar Buhari Dole mu sa kafa mu sa hannu Sai Janar Buhari Mu cicciba dai uwargidan tamu Sai Janar Buhari Mu kaita gaci da hannuwayenmu Sai Janar Buhari Mu fifitata don ta wayemu Sai Janar Buhari Ta hannun shugaba Buharinmu Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Ya Allah ka sanya alheri Sai Janar Buhari Zaben baba ya wuce jari Sai Janar Buhari Kuri’unmu bana babu mai sari Sai Janar Buhari Koko mutum yanzu ya sha mari Sai Janar Buhari Ko kuma ma ya je gidan yari Sai Janar Buhari Allah bbani wanga dan buri Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Don mene ake bidar mulki Sai Janar Buhari Don sata koko don aiki Sai Janar Buhari Jama’a na ta shan uban aiki Sai Janar Buhari Shi ko yana ta kai kudin banki Sai Janar Buhari Ya dinga shiga yana fitar zaki Sai Janar Buhari Har wataran yazan kamar gunki Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Ajiyarsa tana ta shan uban ninki Sai Janar Buhari Kamar waken da yai ta shan taki Sai Janar Buhari Muko muna habo muna miki Sai Janar Buhari Mun bar jaki muna bugun taiki Sai Janar Buhari Hakika kasarmu na jiran wanki Sai Janar Buhari Ko da ya zame ta gun yaki Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Ya ku masu cin amanarmu Sai Janar Buhari Kusan da sani muna da ranarmu Sai Janar Buhari Ko kun kai dila fa kwa barmu Sai Janar Buhari Kuri’armu tana wurin janar dinmu Sai Janar Buhari Shine za mu bai amanarmu Sai Janar Buhari Don mun san fa baya cutarmu Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari To janaral sai ka zo ka dau aniya Sai Janar Buhari Don mun bika sai shirin tafiya Sai Janar Buhari Garin nasara fa ba a jin gajiya Sai Janar Buhari Ko da ba tuwo fa babu miya Sai Janar Buhari Idan Allah ya kai mu can gidan ajiya Sai Janar Buhari Kowa zai sha amma fa ban da giya Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Sai mai gaskiya da adalci Sai Janar Buhari Sai mai son a ba maza ‘yanci Sai Janar Buhari Sai mai son a danne ha’inci Sai Janar Buhari Sai mai kau da masu zalunci Sai Janar Buhari Sai mai rushe ‘yan munafunchi Sai Janar Buhari Sai sojan da ba ya makirci Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Sai janaral uban mazajenmu Sai Janar Buhari Gaka fari kamar takardunmu Sai Janar Buhari Ga ilmi kamar sukul dinmu Sai Janar Buhari Ga karfi kamar hukumarmu Sai Janar Buhari Ga haske kama da nerarmu Sai Janar Buhari Ga tausai irin na kakanmu Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Na gode ubangiji jalla Sai Janar Buhari Kai ka tsare Buhari ba shakka Sai Janar Buhari Ka sanya ubanmu yai shigar sa’a Sai Janar Buhari Ya mulki kasarmu babu tangarda Sai Janar Buhari Dukkan rayuwa ta inganta Sai Janar Buhari Har sai ya zame gaban kowa. Sai Janar Buhari Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Da Allah mu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari Gara mu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari |
Re: Wakar Janar Muhammadu Buhari by MrCrackles(m): 9:02am On Jul 10, 2009 |
WTF is all the gibberish above? |
Re: Wakar Janar Muhammadu Buhari by ikeyman00(m): 9:11am On Jul 10, 2009 |
hmmm na hostage readin pls let him go hahha |
Re: Wakar Janar Muhammadu Buhari by kokoA(m): 10:13am On Jul 10, 2009 |
Re: Wakar Janar Muhammadu Buhari by muhsin(m): 2:40pm On Jul 10, 2009 |
Re: Wakar Janar Muhammadu Buhari by Nobody: 2:57pm On Jul 10, 2009 |
Meaning will be lost in translation!. WTF |
(1) (Reply)
Names Of Ambassadorial Appointees / Apc Lost In Ambode Home Town(epe) / Power Tussle in Nigeria; SEASON 1- GAME OF ThRONE (photo Gallery)
(Go Up)
Sections: politics (1) business autos (1) jobs (1) career education (1) romance computers phones travel sports fashion health religion celebs tv-movies music-radio literature webmasters programming techmarket Links: (1) (2) (3) (4) (5) (6) (7) (8) (9) (10) Nairaland - Copyright © 2005 - 2024 Oluwaseun Osewa. All rights reserved. See How To Advertise. 21 |