₦airaland Forum

Welcome, Guest: Register • Login • With Google • Trending • Recent • New

Stats: 3,345,667 members, 8,518,827 topics. Date: Sunday, 15 November 2026 at 01:04 AM

Toggle theme

Solicitor01313's Posts

Nairaland Forum › Solicitor01313's Profile › Solicitor01313's Posts

1 (of 1 pages)

Islam › Re: Eid-El-Malud: Celebrants Block Road In Gombe State (Photos) by Solicitor01313: 4:41pm On Dec 24, 2015
Dr. Muhd Sani Umar R/lemo
KYAUTAR BIKIN CHIRISMAS: HALAL KO HARAM?
Dayawa musulmi suna tambayar ko ya halatta su karbi kyautar kirtoci a ranar
kirsimeti, musamman wandanda suke zaune lafiya tare da su, ko suke aiki a
guri daya. Ga bayanin da Malamai suka akai:
1. Baya halatta ga musulmi ya nuna farincikinsa da wannan ranar, ta hanyar
aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamancisu.
2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana.
3. Ya halatta ya karbi kautar da za au ba shi a wannan ranar. Kamar yadda ya
halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi wanada ba yankawa ake yi ba.
Kamar kayan marmari.
4. Dalili kuwa shi ne:
A) Baihaqi ya ruwato a cikin littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa,
muhammad bn Sirin ya ce, an kawo wa Ali (ra) kautar idin majusawa Nairuz.
Sai ya ce, menene wannan kuma? Sai suka ce masa, ya sarkin muminai yau
ranar idin Naruz ce. Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Fairuz'. Wato ya karba, tare
da nuna ya ji dadin kyautar.
B) ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu
Barzata Al-Aslamy cewa, yana da makota majusawa, kuma a duk ranar
bukukuwansu suna aiko masa da kaututtuka gidansa, sai yakan cewa iyalinsa,
abin yake kayan marmari ne to ku ci, wanda kuma ba su ba, to ku mayar musu
kayansu.
C) Hakanan ya ruwaito 5/126 cewa, wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce,
muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar
idinsu suna aiko mana da kauta. Sai A'ish (rah) ta ce mata, abin da aka yanka
domin wannan ranar kada ku ci. Ku ci kayan marmari na itatuwa.
Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana
a karbi kyautarsu. Karbar kautarsu a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk
hukunci daya ne, domin wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na
kafirci. Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52. Allah ka shiryar da mu
tafarkinka madaidaici.
5 hrs · Public
Islam › Re: Eid-El-Malud: Celebrants Block Road In Gombe State (Photos) by Solicitor01313: 4:32pm On Dec 24, 2015
ﻭﺗﺸﺮﻉ ﺯﻳﺎﺭﺓ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ ﻟﻼﺗﻌﺎﻅ ﺑﻬﺎ ﻭﺗﺬﻛﺮ ﺍﻻﺧﺮﺓ ﺷﺮﻳﻄﺔ ﺃﻥ ﻻ ﻳﻘﻮﻝ ﻋﻨﺪﻫﺎ ﻣﺎ ﻳﻐﻀﺐ
ﺍﻟﺮﺏ ﺳﺒﺠﺎﻧﻪ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ ﻛﺪﻋﺎﺀ ﺍﻟﻤﻘﺒﻮﺭ ﻭﺍﻻﺳﺘﻐﺎﺛﺔ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﺃﻭ ﺗﺰﻛﻴﺘﻪ ﻭﺍﻟﻘﻄﻊ ﻟﻪ
ﺑﺎﻟﺠﻨﺔ، ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ، ﻭﻓﻴﻪ ﺃﺣﺎﺩﻳﺚ :
ﺍﻷﻭﻝ : ﻋﻦ ﺑﺮﻳﺪﺓ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺼﻴﺐ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ‏(ﺇﻧﻲ

1 (of 1 pages)