Welcome, Guest: Register On Nairaland / LOGIN! / Trending / Recent / New
Stats: 3,215,608 members, 8,026,487 topics. Date: Wednesday, 11 December 2024 at 04:37 PM

Darusan Azumi Game Da Samar Da Al’umma Ta Gari Laccar Jawabi Daga Malamai Ta She - Nairaland / General - Nairaland

Nairaland Forum / Nairaland / General / Darusan Azumi Game Da Samar Da Al’umma Ta Gari Laccar Jawabi Daga Malamai Ta She (2209 Views)

5eun Ti Ta Politics Section Fun Okoro O!!!!! / Seun Se Wa Ta Nairaland / Hukumar Zabe Ta Najeriya Ta Tsayar Da Afrilu Domin Zaben 2011. Wannan Lokacin Ya (2) (3) (4)

(1) (Reply)

Darusan Azumi Game Da Samar Da Al’umma Ta Gari Laccar Jawabi Daga Malamai Ta She by mousty: 3:05pm On Jul 29, 2012
GABATARWA
1. Ana auna al’umma ne da ma’auni guda uku:
i) zamantakewarsu
(ii) tsarin tattalin arzikinsu
(iii) yanayin shugabancinsu.
Idan wadannan abubuwa suka yi kyau, al’umma ta samu nagarta. Idan aka
rasa su, an rasa nagarta.
2. A cikin azumi, da abubuwan da suke ta’allake da shi, an tanadarwa
Musulmi abubuwan nan guda uku.
3. Azumi ya na nufin kamewa daga ci da sha da saduwar aure, daga
fitowar rana zuwa faduwarta, da nufin ibada.
4. Abubuwan da suke taimakawa wajen samar da al’umma ta gari sun hada da :
i) Hadin kai (kaucewa rarrabuwa, tausayin juna, karuwar karfi, cin
nasarar abinda aka sa a gaba)
ii) Zaman lafiya (samar da kwanciyar hankali, Karin lafiyar
jiki,cigaban tattalin arziki)
iii) Tarbiyya (ta na sawa na kasa ya girmama na sama, na sama ya
tausayawa na kasa)
iv) Haduwa don yin ibada (a hadu a tattauna nasarori da matsaloli, a
shawarta mafita, a godewa ni’imomi, a dada kaunar juna)
v) Shugabanci na gari (wanda babu rashawa ba cin hanci, babu magudi,
babu karfa-karfa, babu ‘yar burun-burun)
vi) Tsari mai nagarta ( kamar tafiyar da makarantu, asibitoci,
kasuwanci, da makamantansu, wannan shine baban abinda shugabanci na
gari ya ke samarwa).
5. Azumi yana koyar da duk wadannan, ga mutane masu lura.
AZUMIN RAMADAN DA YADDA YA KE KOYAR DA NAGARTA
Azumin watan Ramadan farilla ne, kamar yadda ya zo a cikin ayoyi shida
a Suratul-Baqara (2: 183 – 188):



Ayah 183:
Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya,an wajabta azumi a kanku kamar
yadda aka wajabta a kan wadanda suka gabace ku [an yi haka ne] don ku
ji tsoron Allah.

DARASI:
hadin kai (tsakanin ku da magabata, da kuma kiranku da aka yi gaba daya);
tsoran Allah (ta hanyar bin dokakinSa, a ibada da mu’amala)
Nagarta (juriya, kunya, sanin ya kamata)
Taka tsan-tsan (kaucewa duk wata barna).

Ayah 184
Yan kwanaki ne kidayayyu; wanda kuwa ya kasance ba shi da lafiya daga
cikinku ko kuwa yana cikin tafiya, (ya sha azumi) sai ya cika adadin
abin da ya sha daga wasu kwanaki. Kuma fansa ta ciyar da miskini tana
kan wadanda suka sha tare da ikon yinsa (da kyar). Wanda ya kara (ita
fansar) don samun lada wannan shi ya fi masa alheri. Amma kuma ku yi
azumin (shi) ya fi alheri a gareku idan kun kasance kun san haka.

DARASI
Muhimmancin saka ajali wajen cimma manufa;
Koyar da juriya da rashin tsoro wajen tinkarar al’amari;
Tsarin kula da masu rauni ya na daga cikin nagartar gwamnati da al’umma;
Muhimmancin fansa da makamantan haka wajen cigaban tattalin arziki;
Fifikon taqawa akan komai. [hadithi ya ce farkon Ramadan rahama,
tsakiyarsa gafara, karshensa ‘yantawa daga wuta].

Ayah 185:
(Wannan shi ne) watan azumi wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa,
don shiriya ga mutane da (ayoyi) mabayyana don shiriya da
rabewa(tsakanin karya da gaskiya). Wanda ya rayu cikinku har zuwa
watan (ko wanda ya san an ga watan) to sai ya azumce shi. Kuma wanda
ya kasance marar lafiya ko a cikin tafiya sai ya yi adadin wasu
kwanakin (daidai yawan wadanda ya sha). Allah Yana nufin sauki ne a
gare ku, kuma ba Yana nufin wahalar da ku ba ne, don ku cika adadin
kwanakin don kuma ku girmama Allah a bisa shiriyar da Ya yi muku, kuma
ku gode (wa ni’imominSa).

DARASI
Mutane sai ana shiryar da su; [a gida, hanya, office, kasuwa,
masana’anta, da wuraren hira]
Muhimmancin hadin kai; [wajen amincewa da ganin wata, ko a ina aka
ganshi; da amincewar umarnin shugaba game da ganin wata]
Muhimmancin kulawa da raunana; [tun da Mahalicci ya tausayawa abinda
ya halitta, kai kuma fa?]
Muhimmancin godiya game da alheri; [wanda ya saba godewa Allah, zai
godewa mutane]
Da rashin manta alheri. [wannan zai sa cin zarafin juna ya yi. sauki].


Ayah 186:
Idan bayina suka tambaye ka game da Ni (ya Muhammadu ka ce da su),
hakika Ni a kusa nake, ina amsa addu’ar mai addu’a idan ya roke Ni,
kuma su nemi na amsa musu kuma su bada gaskiya da Ni don su shiriya.

DARASI
Kusancin Allah da bayinSa; [don haka kada su shagala wajen aikata ba
dai dai ba; kada kuma su manta ko su raina alheri].
Bukatar hada Allah da bayinSa, ba da wani abu daban ba; [shine zai
sa a dauwama cikin shiriya]
Karbar addu’ar bayinSa;
Bukatar yi masa biyayya, wajen yin azumi da aiki da darussan da aka
koya a cikin azumi.

Ayah 187;
An halarta muku tarawa da matayanku a daren azumi; su sutura ne a gare
ku, ku kuma sutura ne a gare su. Ubangiji Ya san cewa hakika kun
kasance kuna ha’intar kanku, sai Ya karbi tubanku kuma Ya yafe muku ba
tare da Ya yi muku azaba ba); to yanzu kwa iya rungumarsu, ku nemi
abin da Allah Ya halatta muku, kuma ku ci ku sha har sai farin kyalle
ya bayyana a gare ku daga bakin kyalle na alfijir; sannan ku cika
azumi zuwa dare. Kada ku rungume su idan kuna lazimin ibada a cikin
masallatai. Wadancan iyakokin Allah ne, to kada ku kusance su. Kamar
haka Allah Ya ke bayyana ayoyinSa ga mutane don su sami taqawa.

DARASI:
Muhimmancin rayuwar aure;
Muhimmancin tsara rayuwa ta mutum ko ta al’umma;
Muhimmancin haihuwa wajen dorewar al’umma;
Dora hukunci gwargwadon yadda mutane za su iya
Muhimmancin bin doka da oda
Maimaita muhimmancin taqawa.

Ayah 188:
Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakanin ku ta hanyar cuta, kuma (kada)
ku bayar da ita ga Mahukunta don ku ci wani yanki na dukiyar mutane ta
(hanyar) cuta, alhali kuwa kuna sane (da cewa) wannan haramun ne.


DARASI
Hani ga cin haram;
Hani ga rashawa da cin hanci;
Hani ga almubazziranci;
• Nuni ga neman halal da alkinta dukiya;
• Nuni ga shugabanci na gari.

WASU ABUBUWAN MASU ALAKA DA AZUMIN RAMADAN
Abubuwan da su ke da alaka da azumin Ramadan:
i) Bude baki(iftar)
ii) Tafseer
iii) Tarawih
iv) Tahajjudi
v) I’itikafi
vi) Zakatul-fitri
vii) Idil-fitri

BUDE-BAKI (IFTAR):
• Koyar da zumunci;
• Da hadin kai;
• Da tausayi;
• Samar da bunkasar ciniki.

TAFSEER:
• Ya na haifar da kai-komo tsakanin jama’a;
• Da sada zumunci;
• Da tunasar da al’umma hakkokin Allah da na mutane da suke kansu;
• Haduwa don ibada;
• Haka ma sallolin tarawih da na tahajjudi da I’itikafi.

TARAWIH:
• Ta na koyar da nafilfili
• Da haduwa al’umma
• Da shiryar da matasa dagewa wajen ibada
TAHAJJUDI:
• Ta na jaddada darusan tarawih
• Ta koyar da tashi yin sallar dare
• Ta dada nesanta mutun da laifuka
I’ITIKAFI:
• Jaddada darusan tahajjudi
• Tarbiyar ruhi
• Inganta zumunta
ZAKATUL-FITRI:
• Rage radadin talauci;
• Samar da daidaito tsakanin jama’a;
• Rage hasada tsakanin mai shi da marar shi.

IDIL-FITRI:
• Samar da annashuwa;
• Da hadin kai;
• Da zumunci;
• Da cigaban yan’uwantaka;
• Da bunkasar ciniki;
• Da nuna karfin Musulunci.

AZUMIN KAFFARA DA NASA DARUSSAN

AZUMIN RANTSUWA: Surah Ma’ida, 89:
Allah ba Ya kama ku da yasassun rantse-rantsenku sai dai Yana kama ku
da abin da kuka kulla rantsuwa a kansa, sannan kaffararsa ita ce ciyar
da miskinai goma daga cikin matsakaicin abin da ku ke ciyar da
iyalanku (da shi), ko tufatar da su, ko kuma ‘yanta wuyaye, sannan
wanda bai sami (yin) wadancan ba sai (ya yi) azumi kwana uku. Wannan
shi ne kaffarar rantsuwarku idan kun rantse. Kamar haka ne Allah Ya ke
bayyana maku ayoyinSa don ku gode.

DARASI:
i) Muhimmancin rantsuwa wajen tarbiyyar mutane;
ii) Kula da raunana a matsayin ci gaban al’umma;
iii) Muhimmancin ‘yanci a rayuwa;
iv) Azumi a matsayin tunasarwa game da wadanda suke cikin wata ukuba.


AZUMIN ZIHARI – Surah Mujadalah, 3&4;
Wadanda kuwa suke yin zihari ga matansu sannan su dawo daga abin da
suka fada, to sai su ‘yanta wuyaye tun kafin su sake saduwa. Wannan
ake yi muku wa’azi da shi. Allah kuma Masani ne da abin da kuke
aikatawa.
Sannan wanda bai samu ba (abin ‘yantawa) sai ya yi azumin wata biyu a
jere tun kafin su sake saduwa. Sannan wanda bai samu iko ba sai ya
ciyar da miskini sittin.Wancan don ku bada gaskiya da Allah da kuma
ManzonSa. Wadancan kuma iyakokin Allah ne, kafirai kuma suna da azaba
mai radadi.

DARASI:
i) ‘Yanci ya fi abinci muhimmanci(a wasu lokuta);
ii) Nuni game da girman iyaye mata;
iii) Azumi ya na tunasarwa game da bukatar ‘yanta mutane;
iv) da tunasarwa game da bukatar yaki da yunwa;
v) Ciyarwa kuma ta na daga cikin dabarar yaki da talauci.

FARAUTA YAYIN AIKIN HAJJI: Surah Ma’ida, 94/5:

Ya ku wadanda kuka bada gaskiya, kada ku kashe abin farauta a halin
kuna (cikin) harami. Duk wanda kuwa ya kashe shi daga cikin ku da
gangan, to ramuwar gwargwadon abinda ya kashe na daga dabbobi (ya
wajaba a kansa); mutum biyu ne kuma adalai daga cikinku za su yi masa
hukunci da shi (ya zamanto kuma) hadaya ce mai isa ka’aba, ko kuma ya
yi kaffarar ci da miskinai, ko kuma ya yi azumi daidai da (yawan
mudunnabin ciyarwa) don ya dandani sakamakon aikinsa. Allah Ya yi
afuwa ga abin da ya shige, wanda kuwa ya sake to Allah zai yi masa
ukuba,
(ga wanda ya saba maSa).

DARASI
i) Muhimmancin doka da oda ga al’umma/zamantakewa;
ii) Muhimmancin horo wajen tabbatar da doka da oda;
iii) Muhimmancin ciyarwa;
iv) Azumi a matsayin tunatarwa game da bukatar kawar da yunwa.

AZUMIN NAFILA DA NASA DARUSSAN
Sitta Shawwal (wajen jumhur, banda Malikiyya);
Ashura ta Tasu’a;
Ayyam al- bid(Raneku uku masu haske, 13,14&15);
Litinin da Alhamis;
Da sauransu.

DARASI
i) Tuni ga azumin Ramadan;
ii) Kasancewa cikin godiya ga Allah;
iii) Neman kusanci ga Mahalicci;
iv) Da kuma duk darussan da ke cikin azumi.
[[
KAMMALAWA
Allah ne kawai Ya barwa kanSa sanin ladan da ke cikin azumi da kuma
tarbiyar cikinsa;
Daga cikin anfanin azumi ga danAdam akwai kyautata zamantakewa da
cigaban tattalin arziki da kuma samar da al’umma ta gari.;
Yadda azumi ya ke tafiya da maganar ciyarwa ya na nuni da
muhimmancin kula da masu rauni a cikin al’umma;
Duk abin da ake bukata na gyaran zamantakewa da tattalin arziki da
shugabanci na gari ya na tattare da azumi.
Allah Ya bamu ikon yin azumi da aiki da darusan da ke cikinsa,
tsawan rayuwarmu.


Wassalamu Alaikum.

(1) (Reply)

Seun Please Ban My Account.... Till The End Of The World / Breaking News: Instant Noodles Cause Heart Attack, Say Researchers. / What Does "Share" Means On Nairaland Threads?

(Go Up)

Sections: politics (1) business autos (1) jobs (1) career education (1) romance computers phones travel sports fashion health
religion celebs tv-movies music-radio literature webmasters programming techmarket

Links: (1) (2) (3) (4) (5) (6) (7) (8) (9) (10)

Nairaland - Copyright © 2005 - 2024 Oluwaseun Osewa. All rights reserved. See How To Advertise. 49
Disclaimer: Every Nairaland member is solely responsible for anything that he/she posts or uploads on Nairaland.