Welcome, Guest: Register On Nairaland / LOGIN! / Trending / Recent / New
Stats: 3,152,987 members, 7,817,905 topics. Date: Saturday, 04 May 2024 at 10:33 PM

Hausa Writers--our Pride - Culture - Nairaland

Nairaland Forum / Nairaland / General / Culture / Hausa Writers--our Pride (5343 Views)

To You,is Kwara State A Yoruba Land Or Hausa? / South South: Nigeria's Pride Through Diversity / Brief History Of Hausa Speaking People. (2) (3) (4)

(1) (Reply)

Hausa Writers--our Pride by Imgombe2016(m): 3:01pm On Jul 16, 2015
Fauziyya D. Sulaiman wadda aka fi
sani da Matar Bello Q far Q an haife
ta a unguwar Fagge a Shekarar 1981
ta yi karatuna na Firamare a
Makarantar Festival Primary School,
daga nan wuce makarantar
‘yammata ta kwana Government
Girls Secondary School ‘Yar gaya a
shekara ta 1993, bayan ta kammala
karatunta na Jiniya ta koma
Makarantar Government Girls
College Dala ta karasa karatunta
daga 1995 zuwa 1998. Daga nan ta
yi aure a shekara ta 1999. A shekara
ta 2003 ta koma karatu a Makarantar
College of Health Sciences, School
of Hygiene in da ta yi Diploma a kan
Assistant Nutritionist. Daga nan ta yi
Certificate a Makarantar School of
Management, akan Hotel and
Catering Services.
A game da rubutu kuwa ta fara
rubuta littafi a shekarar 2002, in da
littafi na farko mai suna Me na yi
mata?. Daga nan ta ci gaba da
rubuta littafi da suka hada da:
Kishin Banza
Guduna Ake yi
Rayuwar ‘Ya Mace
Mece ce Rayuwa
Burin Raina
Karshen Wahala
Labarin Zuciya
Matsalar Mace
Mijin Uwa
Auren Kudi
Duk Abinda Namiji Ya yi
Fauziyya mamba ce a Kungiyar
Marubuta ta Najeriya reshen jihar
Kano kuma tana rike da mukamin
jami’a a majalisar gudanarwa ta
Kungiyar tun watan Maris na 2009
har zuwa 2010. Daga nan aka sake
zabenta a dai wannan mukami daga
watan Maris na 2010 har zuwa
watan Maris na 2012 insha Allah
Quoted from Dr Yusuf N Adamu's blog.Published since 2008.

1 Like

Re: Hausa Writers--our Pride by Imgombe2016(m): 3:16pm On Jul 16, 2015
A wata na karshen shekarar Milladiya ta 1979 aka haifi Kabiru Yusuf Anka a ranar Litinin 1 ga watan Disamba, 1979, a lissafi yanzu yana da shekaru 29 kenan a raye a duniya. Haka nan ya fara da karatun Alkur'ani a bangaren ilimin Arabiyya kenan wanda idan aka hada da makarantar Islamiyya ta Sabilul Rashad da ke Gyadi-gyadi da Mukhtariyya Islamiyya da ke Fagge da kuma Thimarul Qur'an (bangaren dare) ya sami saukar Kur'ani da sauran tarin littattafan Fiqh, Sirah, Nahwu, Tajwid, Hadis da sauransu. Ya yi karatun Firamare a Kurna Special Primary School, dake kan titin Katsina daga nan sai ya wuce karamar sakandire ta JSS Kurna, da kuma makarantar GTC K/ Nassarawa. Bayan kammalawa ya wuce School of Technology, Kano inda ya sami shaidar satifiket a bangaren Electrical Electronic. Ya kuma wuce Jami'ar Bayero ya sami shaidar Diploma a bangaren aikin jarida (Mass Communication) Sha'awar sauya layi a karatu ya sa ya koma makarantar sakandire ta Kwakwaci inda ya yi jarrabawar NECO a 2006. Ya samu shaidar karatun Diploma a bangaren na'ura mai kwakwalwa (Computer) a makarantu biyu: Online Computer da kuma Hands- On Computer Institute inda ya karanci (Desktop Publishing da Data Processing and Maintainence) Kabiru ya kware a wajen sarrafa na'ura mai kwakwalwa musamman a bangaren zane da bugu (design graphics and typing) wanda har shaidar satifiket ya samu a Mavis Beacon Typing Institute a May 5, 2003 da maki 92% (accuracy) Haka nan ya buga littattafai, jaridu da mujallu masu yawa a bugun kwamfiyuta, ya kuma tsara shafukan mujallu da jaridu da kuma tsara bangwayen littattafai da yawa. Marubucin yana da sha'awar aikin jarida da rubuce-rubucen jarida, don haka ya yi aiki a jaridu kamar haka:- Wakiliya -(mujallar Marubuta) - a matsayin mataimakin Edita. Inuwar Marubuta -(mujallar Marubuta) - marubuci na musamman Suda -(mujallar 'yan fim) - marubuci Kwallon Kafa -(mujallar labarun wasanni) -mataimakin Edita. Muryar 'Yanci -(jaridar labaran karamar hukumar Fagge) -Edita Masoya -(mujallar Labaran rayuwa da soyayya) - Edita Kakaki -(mujallar kare ra'ayin karamar hukumar Fagge) -Edita Haka ya yi rubuce-rubuce da dama a jaridu da mujallu na kasar nan. A bangaren kungiyoyin marubuta, Kabiru yana cikin wadannan kungiyoyi:- Hausa Authors Forum (HAF) - Mataimakin Shugaba Association of Nigerian Authors (ANA) Kano - a matsayin sakataren yada labarai na bangaren Hausa (P.R.O. Hausa) Shugaban Gimbiya Publishers. Kabiru ya fara rubuce-rubucen sa tun yana makarantar Firamare aji na hudu, inda shi ne mataimakin shugaban aji, kuma shi ke karanta littattafan Hausa, kamar irin su Magana Jari Ce da sauransu. Wasu daga cikin littattafan da ya wallafa da sunan shi Kabiru Yusuf Anka sune:- 1. Karfin Hali... 2. Shure-shure... 3. Ninkaya 4. Alwashi 5. Bilkisu 6. Firgita Samari... 7. Rayya 8. 'Yan mata... 9. Kushewar Badi... 10. Salo 11. Hadarin Kaka (a daidaita sahu) 12. Launin So 13. Mataye 14. Rauni 15. Rayayye 16. Dansanda.. A bangaren Turanci ya wallafa:- 1. Standard Dictionary/Teach- yourself * 2. Successful Dictionary/Teach- yourself * 3. An Essential Way of Learning English * 4. Learning English 5. My Pen and Others Stories *ma'ana da hadin gwiwar wani suka wallafa Haka nan ya wallafa wasu littattafan da sunan Muhammad Matashi Fagge kamar:- 1. Kalmar So 2. Sakon Masoya 3. Dandalin Soyayya 4. Wasikun Soyayya 5. Dan Soyayya 6. Sarkin Tsari 7. Mallaka 8. Littafin So 9. Birnin Soyayya A yanzu haka yana da aure da 'ya daya mai suna Ummi. Yana da sha'awar ba da umarni a finafinan Hausa, da sha'awar wasan kwallon kafa. Kuma yana kokarin wucewa karatun digirinsa a kasar waje.

1 Like

(1) (Reply)

Yoruba Are 99% Genetically Identical To Igbos, Akan and Gaa-Adangbe - Study / The Esans And Fair Skin / Names Of Animals In Ebira Language :D

(Go Up)

Sections: politics (1) business autos (1) jobs (1) career education (1) romance computers phones travel sports fashion health
religion celebs tv-movies music-radio literature webmasters programming techmarket

Links: (1) (2) (3) (4) (5) (6) (7) (8) (9) (10)

Nairaland - Copyright © 2005 - 2024 Oluwaseun Osewa. All rights reserved. See How To Advertise. 20
Disclaimer: Every Nairaland member is solely responsible for anything that he/she posts or uploads on Nairaland.