Welcome, Guest: Register On Nairaland / LOGIN! / Trending / Recent / New
Stats: 3,154,970 members, 7,825,034 topics. Date: Sunday, 12 May 2024 at 12:47 AM

The Reality Of What Happens At Saudi(minna) In Hausa. - Nairaland / General - Nairaland

Nairaland Forum / Nairaland / General / The Reality Of What Happens At Saudi(minna) In Hausa. (1225 Views)

18-Seater Bus Involved In Accident On Bida-Minna Road, People Dead (Graphic Pics / Corper Ebere Christian Dies In Accident Along Minna Road / Electric Shocks Policeman In Minna And 2 Others (Photos) (2) (3) (4)

(1) (Reply)

The Reality Of What Happens At Saudi(minna) In Hausa. by Kagarko(m): 10:55pm On Sep 30, 2015
Daga Shehin Malamin Sunnah Sheik Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya Dan Allah Ka Daure Ka Karanta, Ka Kuma Turama Wasu Suma Su Karu MUTUWAR SHAHADAR ALHAZAI A WAJEN JIFA DA MAKIRCIN YAN SHIAH (IRAN) Alallh ya mana magininsu da karnukan su. @ Wajibi ne mu zamo masu Taka tsantsan akan fadin maganganu da yada jita, jita, da cin mutunci da kuma kage ga Hukumomin Saudiyya! Akan wannan sha, ani, Mu sani cewa duk abin da muka fada Allah zai tambaye mu.( ﻣﺎ ﻳﻠﻔﻆ ﻣﻦ ﻗﻮﻝ ﺇﻻ ﻟﺪﻳﻪ ﺭﻗﻴﺐ ﻋﺘﻴﺪ ) @ Ina jiye mana Tsoron mu wayi gari muna yiwa yan shi, ah aiki , bamu sani ba ko kuma mun sani. A wannan Harkar , wallahi mutum zai wayi gari ya zama Karen Farautar Iran da shiah duka , bai farga ba. A duk Duniya ba wadanda suka fara fitowa suna Tsinuwa da Batanci ga Kasar Saudiyya akan wannan lamari na mutuwar Alhazan nan sai yanshi, ah, su kuma suna yi ne don Siyasar su da Gina Aqidar su ta Shianci da take Tsananin Fada da Sunnah. @ Duk mai hankali da tunani yasan irin jarimin kokarin da hukumar Saudiyya take yi shekaru da Dama , wajen Taimakawa duniyar musulunci da kai taimakon agaji na Gaggawa ga kasashen musulmi Talakawa da Taimakawa Daliban ilmi , da Kyautata rayuwar Alhazai , da kashe Makudan Dalolin kudi don Gina Haramaini, na Makka da Madina, , a duk Duniya babu babban wuri da yakai tsadar Haramaini, Duk Duniya babu wata Qasar da ta isa tayi wannan in ba saudiyyar ba,! AMMA DUK DA HAKA BAZA, A JINJINA MUSU BA DA KUMA YI MUSU ADDUAR DAUWMA A CIKIN NI, IMA, SAI WANNAN ABU YA FARU , MUTANE BA TARE DA BINCIKKE NA ADALCI BA , SU KAMA SUKA GA SAUDIYYA , SUNA GOYON BAYAN YAN SHIAH?? SUBHANALLAH!!! Babu Alunci daya wuce wannan! Ku tuna fa kwanan nan suka zuba makudan kudi Naira milion 60 na Diyya ga dukkan alhajin daya mutu a Ahrami, akan abin da ma ba laifin su bane Allah ne kawai ya kawo, Ko Ameri report da suka bayar sun wanke saudiyya sunce is Natural deserter ne kawai. @ Yan shia sune musabbabin Hallaka Alhazai a wannan Hatsari, bayan bincike mai zurfi da na gabatar daga kasa mai Tsarki da kuma nan gida Nigeria, da kuma sauran Alhazi da abin ya faru a gaban su, ya tabbata cewa , daman kasar Saudiyya suna da security Report cewa akwai yiwuwar yan shiah bana zasu tada wata babbar Tarzoma a Minna, don haka hukuma ta saka musu kakkarfan tsaro a Hemomin su da sojoji, kuma aka kaiyade musu lokacin da zasu tafi jifa, kada su cakuda da mutane, don gudun Makircin su, amma kash!!! Suka karya wannan Doka suka fita a lokacin da aka hana su, sannan suka fi karfin jamian Tsaron suka wuce sukayi jifan su, sannan suka dawo ta hanyar da ba, a dawowa don mugun nufi ga Al, umma, wannan ya sabbaba mutuwarjama, a da dama harma da tasu jama, ar. WANAN BAYANI HAKA GIDAN TALVITION NA AL ARABIYYA SUKA TABBATAR A JIYA, KOWA YAJI A DUNIYA. @ Ana ta yada cewa Hukumomin Saudiyya sun rufe hanyoyi, to don Allah ya kamata mu tambayi kanmu meye ribar da hukumomin Zasuci don sun rufe hanyoyi Alhazai sun mutu? Haba jama, a ? Ya kamata Mu zurfaf tunani, duk hanyar da aka rufe ta anyi haka ne don sama wa Alhazai saukin Gudanar da aiki ba wai don a cutar dasu ba sam!! @ Abun Bakin ciki wai har wani ya bude baki yace , a kwace Gudanar da aikin Hajji daga hannun Saudiya a maida shi international issue!!! Allah ya saukake, yanzu wace kasa ce ake ganin ta isa tayi wannan Hidimar da akeyi wa Alhazai a duk Duniya in ba saudiyya ba? Mu daina yaudaran kanmu da abin da Kasar iran take yadawa na farfagandar cin mutuncin sunnah da Musulmi gaba daya. NEMA AKEYI AYI ZAGON KASA AKAN HARKAR AIKIN HAJJIN GABA DAYA,. kai kuma baka lura ba za, ayi amfani dakai a cimma wannan majufa mummuna. @ Rubutun dawani mutum yayi a Daily trust ta jumuar da ta gabata, sam! ba akan hanya yake ba, akwai son zuciya da neman bata wassu da gina iyayen gidan sa yan shiah, sanin da yawa daman wannna mutumin kasurgumin dan Shiah ne, kullum rubutun sa na Ranar jumua a Daily Trust, yana nuna haka, matukar yana alaka da addini, shiah kuwa ba yanda zasuyi su kaunaci saudiya, shi yasa baza ka taba ganinsa yayi rubutu yana yabon sunnah ba sam!! Ya kamata Jaridar Daily Trust ta dakatarda saka rubutun wannnan mutumin don kuwa yana Tallata Akidar sa ne kawai a cikin jaridar, in kuma Dailytrust din ta zama ta yan shiah ne to a mana bayani!!! @ A takaice ya jama, a Wajibi ne muyi taka tsantsan da dora laifi kai tsaye ga hukumar saudiyya akan wannan hatsari da ya faru, wadannan mutane wallahi alherin su yafi sharrin su, kowa yasan hakan sai dai son zuciya, wanann Hatsari mafi rinjayen wanda suka sabbab shi yan shia ne, dama suna da muguwar niyya da Gilli akan saudiya, shekara guda sukayi bana basu shiga saudiyya ba, saboda suna cike da Haushin fadan saudiyya da yamen, yanzu bari su shiga su Hargitsa al, amurra. Ya Allah kai mana maganin su amin. ★ALLAH YAJIKAN DUKKAN ALHAZAN MU DA SUKA RASU ALLAH YA KARBI SHAHADAR SU AMIN, MARASA LAFIYAN SU ALLAH YA DAGA KADADAR SU, WANDA SUKA BATA ALLAH YA BAIYANA SU. ★KASAR SAUDIYYA KUMA ALLAH YA SAKA MUSU DA ALHERI AKAN HIDIMAR DA SUKE YIWA ALHAZAI DA DUKKAN MUSULMIN DUNIYA, DA KUMA GINA MASALLATAN HARAMAINI GUDA BIYU, WANNAN IBTILA, I DA YA SAME SU BANA KUMA ALLAH YA SA KAFFARA NE GARE MU GABA DAYA, YA KUMA KARA MUSU FASAHA DA BASIRA AKAN GUDANAR DA WANNAN HARKA TA ALHAZAI, YAYI RIKO DA HANNUNSU AMIN. ★ YAN SHIAH KUMA DA SUKA YADA WANNAN SHARRI ALLAH YA KUNYATA SU YA MAYAR MUSU DA MAKIRCIN SU KANSU AMEEEN.

(1) (Reply)

Join 666 / Help For Men Struggling With Pornography And Masturbation / Export Support & Biz Dev Elopement Services, Get Buyer And Earn Dollars

(Go Up)

Sections: politics (1) business autos (1) jobs (1) career education (1) romance computers phones travel sports fashion health
religion celebs tv-movies music-radio literature webmasters programming techmarket

Links: (1) (2) (3) (4) (5) (6) (7) (8) (9) (10)

Nairaland - Copyright © 2005 - 2024 Oluwaseun Osewa. All rights reserved. See How To Advertise. 16
Disclaimer: Every Nairaland member is solely responsible for anything that he/she posts or uploads on Nairaland.