Welcome, Guest: Register On Nairaland / LOGIN! / Trending / Recent / New
Stats: 3,153,070 members, 7,818,197 topics. Date: Sunday, 05 May 2024 at 10:08 AM

A Hausa Advice To Married Women (a Poem) - Culture - Nairaland

Nairaland Forum / Nairaland / General / Culture / A Hausa Advice To Married Women (a Poem) (1953 Views)

Pedophiles/pederasts Are Behind Feminism Not Heterosexual Married Women / Advice To All Ladies (Photo) (2) (3) (4)

(1) (Reply)

A Hausa Advice To Married Women (a Poem) by Chitumu: 4:22am On Aug 21, 2015
Akwai mata mai tsoron Allah Bata nufin kowa da mugunta
Akwai wata ga barna ga gyara Gata da saukin kai ga cuta
Sai ta ukunsu gadangama kenan Bata nufin gyara sai cuta
Bata nufin hairi ga mijinta Baga kiyoshi,ba ga makwabta
Bata nufin gyara sai barna Sai duk safe ta cuci mijinta Ya tafi office kokuma kanti Bata kara zama dakinta
In mai noma ne ko zage Ya tafi gona, zaure za ta Tana nema taga masu wucewa Wai ita dai suga kyan fuskarta
In taga sunki shiga harkarta Sai kaji tace zata makwabta
Kaji irin halayen mata Munana,manyan, makwadaita
In mace bata da kunya barta Kama da miya,in ba gishirinta
In mace bata raga maka barta Daina nufinta kabar sha'awarta
In mace ta zama bata ragama Ko ka sota, kana kuma kinta
In mace, shashanci ya gameta Ba mai kara ganin kirkinta Bata nufin Allah da Ma'aiki Sai bidi'a ita ke ka gunta Taji ana Biko tai mika Sai kaji tace Biko zata
Ba dangin iya babu na Baba Ko kace ta bari, can zata Wannan mace,ba mace ce ba Dai na nufinta kabar sha'awarta
Natsuwa itace mace,ko yar wace In kaga ba natsuwa,ka bajeta
Kasan mata sun iya karya Sun iya yadda suke shirgata
Ba duk mace ke son addini ba Nufinsu a basu kudi, su bukata
Matar da ta zam bata san Allah ba Ba ta kara zama dakinta Sai ta fito a tashar Takatale Sai tai batsa gaban kanwarta
In kace mata, wance ki lura Baka hana ni bugun cinyata
Babu ruwanta da kunya faufau Ga Ashar, ko ciwake yana kunyarta
Sanarwata itace ga mazaje Kar a yawaita kwadai, a takaita
Aure ba abu ne ba na wasa Bar neman kyau, nemi nagarta
Ni nasan mace, komi kyaunta Indai babu hali da nagarta Kana sha'awarta, kana kuma sonta Badan Allah ba kana kyale ta
Don haka, tun farko ka tsaya tsaf! Kai nazari da irin halinta In mace ta zama, shagiri girbau Ko ka aureta, baka iyata. Kun ji mazaje, kar ku kiya man Ku lura da duk farkon maganata
Akwai mata na nan su shidda Zo kusa inna fada ka jimilta
Akwai dibgau! Mai dibge mijinta Ba ta jira ga fada shi taya ta
Danbago, mai zurfin tumbi Ba ta takowa sai ta cikinta
Sai shirwa ita dai tayi fige Kan ta shigo daki sai ta sata
Ratata, sarkin magana ce Tun daga nesa, kana jin kanta
In maganar mace tayi yawa, kaji Tun daga nesa, kana jin kanta
Wannan mata, tayi hasara Sai a nada mata sarki wauta Sai
Malali, ita dai tayi kwance Ta ki ta tashi, ta nemi na kanta
Ba ta kadi, kuma bata sanaá Sai na mijinta, ya bata, ta sata
Sai ta cikon shida, mai mulkin kai Ba mai sa ta, bare shi hana ta
Aure ne, ni nis sa kaina In ka matsa mani, in tafiyata
To shida ta cika ban kara ba Akwai saura, amma na takaita
Akwai saura, amma na kaita Ka shaida akwai mata masu kazanta
In mace ta zam bata da tsafta wannan kam, ta cuci mijinta
Yin tsafta, ta jiki da tufafi Shine ke hana yadon cuta
Wadda ta zam, bata wanke tufa ba Shike shaida, anga kazanta
Zani tuna muku in kun manta Kashedi, da mata masu kazanta
Sun gaza wanke tufa da tukwane Sun ki kula da abinci su kyauta
Ta gaza share cikin dakinta Balle na mijinta, bale fuskatta
Kun ji isharata ku kiyaye Ku lura da duk farkon maganata
Akwai barna ga mazaje Zamu fada musu, don su raga ta
Wadansu maza dauka da ajewa Sun dauko mace, sai su aje ta
Ba laifin tsaye, babu na zaune Sai kaga basu zuwa dakinta
Ran aikinta ba zai fara'a ba Ko magana tai, bashi kulawa
Duk namijin da ya dau kwanan wata In ya hana mata, don bai son ta
Yaki batun Allah da maáiki ya kashe kansa, saboda mugunta
Mata gunku amanar Allah ce Don Allah maza ku rike ta
In mace tai maka laifi daure Sai ka tuna, ai kai ka aje ta
Su mata halinsu mugunta Sai dai-dai ke, basu da keta
Macce, mijinta ko sarki ne bata yaba masa, sai in bata
Macce mijinta ko malam ne Bata yabonsa tace da nagarta
Tana iya cewa miji mataulaci Koda yayi kudin Dantata
Su ka bugu su riga kai kara Ba ai magana ba su je su tsirata
Macce tana shiryawa mijinta Karya, don ya bari tayi cuta
Tâce mashi zata gidan kanwarta Ko kuma zata ta gaida uwaye
Ta fita, ta samu ta sulale Ta shiga yawo santa-santa
Ba ta gidan iya, bata na Baba Kaji nufinta ta sheke ayarta
Don haka mata, ba'a iya musu In kaji sun magana ka aje ta
Kowace mata na da halinta Wadansu da kyau, wasu ko da mugunta
Wata in suka fara fada da mijinta Sai ta rike shi, tace ya kasheta
In kuma yaki ta kama tufarsa Ace ta sake shi, tace ya kasheta
Ko kuma yanzu ka bani takarda In kuma ka ban in ketata
In kuma kace anshi takardar Sai kaji tace, bani riketa
Ita dai sababi ta ka so ta aza mai Indai yace bashi sakinta
In ka hada ta da Allah sannan Tafi matsa maka don tsiwarta
Kai kuma gaka kana jin kunya Ga shari'a ka zage ka kasheta
Don haka sai kowa yayi sannu Ya nemi hali mai kyau da nagarta
Ba'a sayan mota don kyanta Sai kaya, da gudu, da nagarta
To haka ne mace, komi kyaunta. Indai babu hali da nagarta Kamar mota take komi kyaunta Indai ba tafiya, bari sonta
Kyan ladabin mace tai wa mijinta In taki ya mishi, ta kashe kanta
Kui ladabi mata ku kiyaye aure ba'a gama shi da bauta
In mace tai ladabi ta kiyaye Allah sarki, shi ka biyanta
Ku mata ku jiya, ku kiyaye In kuma kun ki, kui mahukunta
Ran mutuwa, da gamo, da kasawa Sai a tuna maka, in ka mance
In mace tabi mijinta da gaske Tayi hakuri ta tsaya dakinta
Bata ganin wani banda mijinta Allah zai mata, babbar kyauta
Miji babban abune bi mjinki Dai na ganin waccan da mijinta
Bishi, ki so shi, ki bar raina shi Ko shine sarkin matalauta
Don ki sani Allah ya aza mai Shi aza masi, shi zai kyauta
Shi abu duk aikin Allah ne Allah shike bada wadata
Ya kasa bayi fanni-fanni Shi yai ma'azurta, yai matalauta
In niyyarki gudun matalauta Sai ya so sannan ki wadata
Shi Allah ba ai masa wayo Yanda yaso, haka za shi hukunta
Ki hakuri ki tsaya ga mijinki In ya wadatu, sai ki wadata

1 Like

(1) (Reply)

Dressing Habit / Pictures From The Coronation Of The Oba Of Benin. Oba Ewuare II / The Mangbetu Tribe In Africa. pics!!!!

(Go Up)

Sections: politics (1) business autos (1) jobs (1) career education (1) romance computers phones travel sports fashion health
religion celebs tv-movies music-radio literature webmasters programming techmarket

Links: (1) (2) (3) (4) (5) (6) (7) (8) (9) (10)

Nairaland - Copyright © 2005 - 2024 Oluwaseun Osewa. All rights reserved. See How To Advertise. 28
Disclaimer: Every Nairaland member is solely responsible for anything that he/she posts or uploads on Nairaland.