Welcome, Guest: Register On Nairaland / LOGIN! / Trending / Recent / NewStats: 3,150,590 members, 7,809,140 topics. Date: Friday, 26 April 2024 at 01:00 AM |
Nairaland Forum / Nairaland / General / Religion / Islam for Muslims / Ma’ana Da Illolin Zina Da Luwadi Damadigo Da Kuma Hukuncinsu (3652 Views)
Major Causes Of Zina (fornication) / Ruling On Zina ( Fornication / Adultery) In Islam / Mut'ah(temporary Mariage) : Zina(adultery) of highest Order (2) (3) (4)
(1) (Reply)
Ma’ana Da Illolin Zina Da Luwadi Damadigo Da Kuma Hukuncinsu by QasimAMuhammad(m): 10:09pm On Nov 24, 2015 |
Ma’ana da illolin zina da luwadi
damadigo da kuma hukuncinsu
Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi
(S.A.W) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Shirka da Allah
alhali Shi ne Ya halicce ka.” Sai aka ce ‘sai
wane?’ Sai ya ce, “Sannan kashe danka don
kada ya ci tare da kai.” Sai aka ce “sannan sai
wane?” Sai ya ce, “Ka yi zina da matar
makwabcinka.” (Bukhari).
Allah Madaukakin sarki Ya sanya hukuncin
wanda duk ya yi zina kuma ya taba aure, a jefe
shi, namiji ko mace; idan kuwa bai taba aure
ba, sai a yi masa bulala dari, sannan a
bakuntar da shi a wani gari daban tsawon
shekara guda.
Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah
Ya kebance shi da wasu abubuwa masu yawa,
saboda munin zina. Ga kadan daga cikin
abubuwan da hukuncin ya kunsa:
•Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta hanyar
jefewa. Ko kuma bulala da bakuntarwa shekara
guda.
•Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya
yayin da ake musu ukuba. Allah Ya ce :
“Mazinaciya da mazinaci ku yi wa kowane
daya daga cikinsu bulala dari. Kada ku ji
tausayinsu a cikin addinin Allah, in dai kun yi
imani da Allah da ranar karshe” . (Annur : 2).
•Yi musu ukuba a gaban mutane, ba a yarda a
yi musu a boye ba, Allah Ya ce :
“Wasu bangare na muminai su halarci wajen yi
musu ukuba (haddi)”. (Annur :2).
Duk wadannan abubuwa suna nuna mana
munin zina da rashin kyanta a Musulunci.
Imamul Bukhari ya kawo, a cikin ingantaccen
littafinsa, daga Maimun Al-audiy ya ce, “A
lokacin jahiliyya na taba ganin wani biri da ya
yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka
taru suka jefe su”.
Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da
mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda
zai yi da matar makwabcinsa. Allah Ya kare
mu.
Illolin Zina: Babu ko shakka duk mai hankali ya
san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa,
wadanda suke shafar mazinacin ko
mazinaciyar, ko su shafi al’umma gaba daya.
Ga wasu daga cikin illolinta :
1. Zubar da mutunci da jawo wa kai kaskanci:
Duk matar da ta yi zina to ta jawo wa kanta da
danginta da mijinta kaskanci, ta kuma zubar
musu da mutunci a idon duniya. Idan har ta
sami ciki ta haihu, sannan ta kashe dan, to ta
hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai. In
kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta
ko danginta, wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa
mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo
mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata
duniya ne
gaba daya.
2. Zina ta hada dukkan sharri gaba daya:
Saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah;
rashin kunya; rashin tsantseni; rashin cika
alkawari; karya da butulci da sauransu. Duk
kuwa wadannan munanan halaye a Musulunci.
Ta’aliki: Mukalar kalmomin “Taala” da “Amin” a
sallama Daga Alhaji Ahmad Muhammadil’Amin
(Bawalle)
Dukkan godiya da yabo suna kara tabbatuwa
ga aninihin Mai su, Ubangiji, kuma makagin
kowa da komai ALLAH – Tabaraka wata’ala.
Mahallicin mutum Ya sanar da shi (mutun)
abin da bai sani ba. Dadin tsiran amincin Allah
su ci gaba da karuwa ga mafificin halitta,
shugaban dukkan Annabawa da Manzanni tare
da zuri’arsa tsarkaka bai daya.
A ranar Juma’a 18 ga Muharram 1432, ina
ofishina a Ma’ahd, wani dalibi ya zo min da
jaridar Aminiya, ya ce “ga jaridar nan, lallai
tunda marubucin ya nemi a shiryar da shi,
baccin an karanta makalarsa, to ka yi rubutu a
kai, kuma wannan maudu’in ya zama shi za ka
yi mana ta’liki a ranar Laraba a ma’ahd domin
tahdib.” Sai na ce tun da a kan shak’wa ce
ilmiyyah, zan rubuta – in Allah (TWT) Ya so -
domin na ga shi marubucin na magana ne a
kan hujja kuma ai kowa ya san cewa HUJJA
MAKAMIN AHLIL – ZIKR ne.
Mai karatu karimi, ina farawa da jawo hankalin
duk wanda zai yi jawabi da sunan Musulunci,
to, ya yi taka-tsan- tsan, ya ga cewa Zatin
Allah ya nufa, kana da tawali’u irin na
marubucin a makalarsa. Hujjojinsa su zama
daga kitabu, sunnah, babu gociya, baudiya ko
kwana, balle fadin son rai don wata manufa
tasa, saboda hadarin da ke tattare da yi hakan.
Shi kuma mai hadisi, ijtihadinsa, in ya yi
sawaba, ajraini, in kuwa akasin haka, ajrun
wahid. Amin. Sai dai na ji dadin fahimtar cewa
marubucin makalar ba yana jayayyar daukakar
Allah ba ne, ko kuma bai yarda sallama ba
fatan alheri ce ba, la la, shi dai a gurinshi ba su
da mazauni, gurin yin sallamar ko amsawa. To
wannan matsalar ba karama ce ba, tana da
fadin gaske, zan raba ta kashi biyu insha’Allah
(TWT). Na farko nunasshe da shi cewa duk
hujjojinsa na Hadisai 5 ba su tsaya a kan
yadda ake yin sallama da mayar da ita kawai
ba. Kuma, kamar yadda ya nemi tabbatattun
hujjoji na yiwuwar a saka kalmomin, to ga
nema a gare shi ta hanyar tambayar - shin in
Annabi bai yi ba, yana hukunta cewa kada a yi
wani aikin ne? Amsa ita ce, Annabi bai yi ba, ba
hujja ba ce, Annabi ya hana, ita ce hujja. Kash,
sai ga shi M. Ahmad bai taimaka wa dalibai
irinmu da Hadisi
ko da rarruana ne inda Ma’aiki ya hana a ce
“Ta’ ala” ko “Amin”, a mas’alar sallama.
Ke nan za mu fahimci cewa yin abu a da’irar
Islama yana zama muhdatha ce in har ba ya
cikin Ayyukan Islama, amman ko da Annabi bai
yi ba, shari’ar Islama ta tabbatar da samun
sararin yi a Ayyukan Ibadan.
Misali:- Ingantaccen Hadisin da Imam Muslim
ya ruwaito a Kitabus salati, Babu fadlul Duhuri
Billail wan-nahar/ wa fadlul Duhuri Ba’dal
Wudu’i (Hadith na 1149) da sahihih Muslim
Babu Min Fadlul Bilal (Hadith 6,609) inda suka
tabbatar cewa Annabi (S.A.W) bai yi wani aiki
ba, amman sai ga shi Bila Babban Bawa, ya bai
wa Ma’aiki amsa cewa shi a duk lokacin da ya
dawwama da tsarki, in har yana da alwala, sai
ya yi nafila raka’a biyu. Annabi bai ce masa me
ya sa ka yi abin
da ban yi ba, kuma ban sa ka ba. Sai kawai ya
tabbatar cewa yana jin motsin takalmin Bilal a
gabanshi, a aljanna. 1 Like 1 Share |
Re: Ma’ana Da Illolin Zina Da Luwadi Damadigo Da Kuma Hukuncinsu by Fundamentalist: 9:42am On Nov 27, 2015 |
we understand you speak hausa very well. please learn to write in english to reach a wider audience |
Re: Ma’ana Da Illolin Zina Da Luwadi Damadigo Da Kuma Hukuncinsu by arabianights: 12:41pm On Dec 04, 2015 |
Is it actually your intention to spread knowledge or to simply amuse your self by seeking for notice?Then you decided to do that in apage created for muslims to learn and educate one another? Be careful 1 Like |
(1) (Reply)
Jarus & Olabowale: Why Is Islamic Teaching And Belief Not Uniform? / Beating In Islamic School / The Importance Of Tajweed
(Go Up)
Sections: politics (1) business autos (1) jobs (1) career education (1) romance computers phones travel sports fashion health religion celebs tv-movies music-radio literature webmasters programming techmarket Links: (1) (2) (3) (4) (5) (6) (7) (8) (9) (10) Nairaland - Copyright © 2005 - 2024 Oluwaseun Osewa. All rights reserved. See How To Advertise. 18 |