Welcome, Guest: Register On Nairaland / LOGIN! / Trending / Recent / NewStats: 3,195,017 members, 7,956,771 topics. Date: Monday, 23 September 2024 at 06:33 PM |
Nairaland Forum / Nairaland / General / Culture / Hausa Writers--our Pride (5418 Views)
To You,is Kwara State A Yoruba Land Or Hausa? / South South: Nigeria's Pride Through Diversity / Brief History Of Hausa Speaking People. (2) (3) (4)
(1) (Reply)
Hausa Writers--our Pride by Imgombe2016(m): 3:01pm On Jul 16, 2015 |
Fauziyya D. Sulaiman wadda aka fi sani da Matar Bello Q far Q an haife ta a unguwar Fagge a Shekarar 1981 ta yi karatuna na Firamare a Makarantar Festival Primary School, daga nan wuce makarantar ‘yammata ta kwana Government Girls Secondary School ‘Yar gaya a shekara ta 1993, bayan ta kammala karatunta na Jiniya ta koma Makarantar Government Girls College Dala ta karasa karatunta daga 1995 zuwa 1998. Daga nan ta yi aure a shekara ta 1999. A shekara ta 2003 ta koma karatu a Makarantar College of Health Sciences, School of Hygiene in da ta yi Diploma a kan Assistant Nutritionist. Daga nan ta yi Certificate a Makarantar School of Management, akan Hotel and Catering Services. A game da rubutu kuwa ta fara rubuta littafi a shekarar 2002, in da littafi na farko mai suna Me na yi mata?. Daga nan ta ci gaba da rubuta littafi da suka hada da: Kishin Banza Guduna Ake yi Rayuwar ‘Ya Mace Mece ce Rayuwa Burin Raina Karshen Wahala Labarin Zuciya Matsalar Mace Mijin Uwa Auren Kudi Duk Abinda Namiji Ya yi Fauziyya mamba ce a Kungiyar Marubuta ta Najeriya reshen jihar Kano kuma tana rike da mukamin jami’a a majalisar gudanarwa ta Kungiyar tun watan Maris na 2009 har zuwa 2010. Daga nan aka sake zabenta a dai wannan mukami daga watan Maris na 2010 har zuwa watan Maris na 2012 insha Allah Quoted from Dr Yusuf N Adamu's blog.Published since 2008. 1 Like
|
Re: Hausa Writers--our Pride by Imgombe2016(m): 3:16pm On Jul 16, 2015 |
A wata na karshen shekarar
Milladiya ta 1979 aka haifi Kabiru
Yusuf Anka a ranar Litinin 1 ga
watan Disamba, 1979, a lissafi yanzu
yana da shekaru 29 kenan a raye a
duniya.
Haka nan ya fara da karatun
Alkur'ani a bangaren ilimin Arabiyya
kenan wanda idan aka hada da
makarantar Islamiyya ta Sabilul
Rashad da ke Gyadi-gyadi da
Mukhtariyya Islamiyya da ke Fagge
da kuma Thimarul Qur'an
(bangaren dare) ya sami saukar
Kur'ani da sauran tarin littattafan
Fiqh, Sirah, Nahwu, Tajwid, Hadis da
sauransu.
Ya yi karatun Firamare a Kurna
Special Primary School, dake kan
titin Katsina daga nan sai ya wuce
karamar sakandire ta JSS Kurna, da
kuma makarantar GTC K/
Nassarawa. Bayan kammalawa ya
wuce School of Technology, Kano
inda ya sami shaidar satifiket a
bangaren Electrical Electronic. Ya
kuma wuce Jami'ar Bayero ya sami
shaidar Diploma a bangaren aikin
jarida (Mass Communication)
Sha'awar sauya layi a karatu ya sa ya
koma makarantar sakandire ta
Kwakwaci inda ya yi jarrabawar
NECO a 2006.
Ya samu shaidar karatun Diploma a
bangaren na'ura mai kwakwalwa
(Computer) a makarantu biyu:
Online Computer da kuma Hands-
On Computer Institute inda ya
karanci (Desktop Publishing da Data
Processing and Maintainence)
Kabiru ya kware a wajen sarrafa
na'ura mai kwakwalwa musamman
a bangaren zane da bugu (design
graphics and typing) wanda har
shaidar satifiket ya samu a Mavis
Beacon Typing Institute a May 5,
2003 da maki 92% (accuracy)
Haka nan ya buga littattafai, jaridu
da mujallu masu yawa a bugun
kwamfiyuta, ya kuma tsara shafukan
mujallu da jaridu da kuma tsara
bangwayen littattafai da yawa.
Marubucin yana da sha'awar aikin
jarida da rubuce-rubucen jarida,
don haka ya yi aiki a jaridu kamar
haka:-
Wakiliya -(mujallar Marubuta) - a
matsayin mataimakin Edita.
Inuwar Marubuta -(mujallar
Marubuta) - marubuci na
musamman
Suda -(mujallar 'yan fim) - marubuci
Kwallon Kafa -(mujallar labarun
wasanni) -mataimakin Edita.
Muryar 'Yanci -(jaridar labaran
karamar hukumar Fagge) -Edita
Masoya -(mujallar Labaran rayuwa
da soyayya) - Edita
Kakaki -(mujallar kare ra'ayin
karamar hukumar Fagge) -Edita
Haka ya yi rubuce-rubuce da dama
a jaridu da mujallu na kasar nan.
A bangaren kungiyoyin marubuta,
Kabiru yana cikin wadannan
kungiyoyi:-
Hausa Authors Forum (HAF) -
Mataimakin Shugaba
Association of Nigerian Authors
(ANA) Kano - a matsayin sakataren
yada labarai na bangaren Hausa
(P.R.O. Hausa)
Shugaban Gimbiya Publishers.
Kabiru ya fara rubuce-rubucen sa
tun yana makarantar Firamare aji na
hudu, inda shi ne mataimakin
shugaban aji, kuma shi ke karanta
littattafan Hausa, kamar irin su
Magana Jari Ce da sauransu. Wasu
daga cikin littattafan da ya wallafa da
sunan shi Kabiru Yusuf Anka sune:-
1. Karfin Hali...
2. Shure-shure...
3. Ninkaya
4. Alwashi
5. Bilkisu
6. Firgita Samari...
7. Rayya
8. 'Yan mata...
9. Kushewar Badi...
10. Salo
11. Hadarin Kaka (a daidaita sahu)
12. Launin So
13. Mataye
14. Rauni
15. Rayayye
16. Dansanda..
A bangaren Turanci ya wallafa:-
1. Standard Dictionary/Teach-
yourself *
2. Successful Dictionary/Teach-
yourself *
3. An Essential Way of Learning
English *
4. Learning English
5. My Pen and Others Stories
*ma'ana da hadin gwiwar wani
suka wallafa
Haka nan ya wallafa wasu littattafan
da sunan Muhammad Matashi
Fagge kamar:-
1. Kalmar So
2. Sakon Masoya
3. Dandalin Soyayya
4. Wasikun Soyayya
5. Dan Soyayya
6. Sarkin Tsari
7. Mallaka
8. Littafin So
9. Birnin Soyayya
A yanzu haka yana da aure da 'ya
daya mai suna Ummi. Yana da
sha'awar ba da umarni a finafinan
Hausa, da sha'awar wasan kwallon
kafa. Kuma yana kokarin wucewa
karatun digirinsa a kasar waje. 1 Like
|
(1) (Reply)
Relationship Between Itsekiri And Igbo / (photos) Naked People Still Exist In Anambra / Traditional Music From Your Respective West African Culture
(Go Up)
Sections: politics (1) business autos (1) jobs (1) career education (1) romance computers phones travel sports fashion health religion celebs tv-movies music-radio literature webmasters programming techmarket Links: (1) (2) (3) (4) (5) (6) (7) (8) (9) (10) Nairaland - Copyright © 2005 - 2024 Oluwaseun Osewa. All rights reserved. See How To Advertise. 35 |